A Najeriya mutane masu lalura ta musamman suna ci gaba da kokawa akan abinda suka kira halin ko-oho da ake nuna musu duk da fafatukar da suke yi ta samun kulawar hukumomi.
Wannan na zuwa ne lokacin da Jihohin kasar ke jan kafa wajen samarwa da aiwatar da dokokin kare hakkokin su.
Tun a shekarar 2019 ne gwamnatin Najeriya ta Santa hannu ga dokar kare hakkokin mutane masu lalura ta musamman tare da umurtar Jihohi da su samar da dokokin a Jihohin su.
Sai dai har yanzu jihohi kalilan ne suka samar da wadannan dokokin abinda yasa masu lalular ke ganin ba'a mahukumta basu damu da su ba.
Wasu masu lalura sun tattauna da Muryar Amurka, inda su ka yi ta bayyana irin matsalolin da al'ummarsu ke fama da su.
Masu fafatukar fadakarwa akan kula da wadannan mutanen na ci gaba da jawo hankulan jama'a da hukumomi akan kulawa da hakkokin masu lalurar.
Dangane korafin cewa kungiyoyi kare hakkin bil'adama suna saku saku da bukatun masu lalura ta musamman kuwa na tuntubi dan rajin kare hakkin bil'adama.
Wasu daga Jihohin da suka samar da dokokin kare hakkin mutanen kamar jihar Sakkwato, har yanzu ana jan kafa wajen samar da hujumomi da zasu kula da lamurran su yadda ya kamata, sai dai gwamnan Sakkwato yace gwamnati na sane da bukatar hakan
Jama'a dai na ganin cewa yana da kyau hukumomi su kula da mutane masu lalura ta musamman ko don gudunmuwar da suke bayar wa a lokutan zabe duk da wahalhalun da suke fuskanta.
Saurari rahoton Muhammadu Nasir: