A yau ne ranar tunawa da wadanda ke dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS a duk fadin duniya,ranar da hukumar kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware.
Komarad Nuhu Sulaiman Gaya shugaban kungiyar masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki ta jihar kano, ya bayyana wannan rana a matsayin ranace da aka yiwa taken tsayadda tsangwama da tsana wato ya dawo an dainayi baki daya.
Ya kuma bayyana cewa kungiyar na cigaba da aiki wajen ilmintar da kuma wayar da kan al’umma kan daina tsangwamar masu dauke da wannan larurar, domin tsangwama na daya daga cikin abin da yake sa wannan larurar take karuwa, rashin tsangwamar kuma na iya rage yaduwar cutar.
Matsalolin da kungiyar ke fuskanta shine rashin kayan gwaje gwaje, da taimako daga kananan hukumomi ga irin wadannan kunguyoyi. Shugaban kungiyar dai ya bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki da su taimaka musu domin kawo karshen wannan cuta a jihar Kano.