Sha-hudu ga watan Nuwambar kowacce shekara, rana ce da aka ware tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO don yin waiwaye kan halin da masu cutar suga ke ciki.
A ranar irin wannan, akan duba matakan kare kamuwa da cutar da kuma matakan da ake dauka wajen yin maganinta.
Cutar suga kan haifar da makanta, mutuwar koda, matsalar zuciya, shanyewar barin jiki, a wasu lokuta ma har ta kan kai ga yanke gabar jiki.
Akan yi maganin cutar ko a jinkirta faruwarta ta hanyar yawan yin gwaji akai-akai.
Akan yawan ba masu dauke da cutar shawarar su rika yin gwajin lafiyar koda, idanu da lafiyar kafa.
Daina shan tabar sigari, na taimaka wa wajen rage yiwuwar kamuwa da nau’in cutar suga mai mataki na biyu da kashi 30-40 cikin 100.
Taken wannan shekara ta 2023 shi ne “samar da hanyar da masu cutar za su samu kulawa.”
Dandalin Mu Tattauna