Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuwar Nelson Mandela A Takaice


Wata 'yar shekara biyu da hoton Nelson Mandela
Wata 'yar shekara biyu da hoton Nelson Mandela

Jiya Alhamis Allah Ya dauki ran tsohon shugaban kasar Afirka Ta Kudu Nelson Mandela wanda shi ne bakin fata na farko da zai shugabanci kasar a tafarkin dimokradiya


YAYIN DA YAKE RANTSUWAR KAMA AIKI A MATSAYIN SHUGABAN KASA

(NELSON MANDELA SWORN IN AS PRESIDENT)
"Ni Nelson Rolihlahla Mandela na rantse zan yi biyaya
ga Jamhuriyar Afirka Ta Kudu, Allah Ka Taimakeni"

Ga mutane da yawa jarumi ne-mutum maikarfin hali da hangen nesa.
A kan ce mutum ne mai saukin kai mai jawo mutane
mai biyayya wanda kuma ya damu da sauran mutane.

An haifi Nelson Mandela ranar 18 ga watan Juli shekarar 1918.
Ya girma a Transkei wurin da aka kebe ma bakaken fata.

Lokacin da yake saurayi ya ya yi kokari cikin
kungiyar dake gwagwarmaya da wariyar launi.
Kana ya shiga kungiyar African National Congress
ko ANC a takaice a wajejen shekarar 1940.
Ya kuma zama shugaban bangaren matasa na jam'iyyar.

Mr. Mandela ya shiga jami'ar inda ya karanta ilimin
fannin shari'a tare da takwaransa cikin ANC Oliver Tambo .
Su ne suka fara bude ofishin lauyoyi na bakake a Afirka Ta Kudu.
Sun kafa ofishinsu a cikin Johannesburg inda suka rika baiwa bakake
shawarwari dangane da shar'ia
ba tare da cajin kudi ba musamman ga marasa karfi ko kuma kudi kalilan.

Gwamnatin wariyar launi ta haramta kungiyar ANC
a shekarar 1960 amma kungiyar ta cigaba a asirce.
Lokacin Mr. Mandela ya yi ta kokarin kauce ma 'yansanda
lamarin da ya tilasta masa tarewa daban
daga matarsa ta biyu Winnie.
Ita ma daga baya ta shiga kungiyar gwagwarmaya
da mulkin wariyar launi.

Lokacin da ANC ta kudiri aniyar fitowa gadan gadan
domin kawo karshen mulkin wariyar launi,
Mr Mandela ne ya shugabanci bangaren soji
yana kula da shiryawa
sojojin Afirka Ta Kudu makarkashiya da kai hari kan wasu sansani gwamnati.

A shekarar 1962 aka kama Mr. Mandela aka gurfanar da shi gaban shari'a
domin abubuwan da ya yiwa gwamnati.
Ya kare kanshi da cewa abubuwan da ya yi
suna cikin fafitikar 'yan Afirka domin su kwato 'yancin kasarsu.

Bayan an yi shekaru biyu ana shari'ar an yanke mashi hukunci daurin rai da rai.
An kaishi wani gidan kaso a tsibirin Robben bayan tekun Cape Coast.
Ya kwashe shekaru 18 a wannan mugun gidan kason.
A wurin ne yaki karbar tayin saki
da gwamnati ta yi masa a shekarar 1989 idan ya yadda tare da ANC ya daina gwagwarmaya.

Amma a shekarar 1990 an sakeshi bayan da gwamnati Shugaba Frederik de Klerk ta halatta duk kungiyoyin siyasa
ta kuma saki frisinonin siyasa.

A shekara 1991 an zabi Mr. Mandela shugaban ANC.
A shekara 1994 yayin da ANC ta lashe
zaben farko da aka yi wanda ya bar duk al'ummar kasar yin zabe,
sai ya zama shugaban kasar bakin fata na farko yana da shekaru 75.

(NELSON MANDELA)

Har abada a wanna kasa tamu mai kyau babu wani da zai sake shan danniya daga wani

(HERMAN COHEN, FORMER ASSISTANT SECRETARY OF STATE)

Herman Cohen tsohon mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka daga 1989 zuwa 1991
ya ce yawancin bakaken Afirka Ta Kudu suna kallon Mr. Mandela a matsayin mutumin da zai kyautata rayuwarsu..

Shugaba Mandela ya ce zai yi wa'adi daya ne kawai.
Mr. Cohen ya ce shekaru biyar din da Mr. Mandela ya yi yana shugabanci
ya samar ma Afirka Ta Kudu bangirma daga kasashen duniya domin daidaituwa da ya kawo wa kasar.

(HERMAN COHEN FORMER ASSISTANT US SECRTARY OF STATE)

"Mr. Mandela ya sadakar da kansa wurin shawo kan 'yan Afirka ga sabuwar akidar
yin aiki domin kawo cigaban tattalin arziki da samun ingantacen ilimi.
Yana kuma kan gaba
wurin fada a ji a duniya.

Wayancin rayuwarsu a matsayin mata da miji,
Winnie da Mandela sun cigaba da zama tare bayan
an sako shi daga tsibirin Robben.
To sai dai daga bisani sun rabu.
Ranar da ya cika shekara 80
Mr. Mandela ya auri Graca Michel
matar marigayi shugaban kasar Mozambic Samora Machel.

Mr. Mandela ya samu daruruwan lambobnin yabo a rayuwarsa.
Ya taba raba lambar yabo da tsohon makiyinsa Mr.de Klerk
An karamasu domin taimakon da suka yi wurin kawo zaman lafiya a Afirka Ta Kudu.
Mandela ya yabawa al'ummar Afirka Ta Kudu.

(NELSON MANDELA)

Kun kirkiro alumma da ta amince cewa mutane daya suke. Babu wanda ya fi wani.

Yayin da yake shugabanci an zargeshi da rashin dakile
yaduwar ciwon kanjamau a Afirka Ta Kudu.
Amma daga karshe ya fito fili yana karfafa yakar cutar.

(NELSON MANDELA)

Tare zamu iya yakar cutar kanjamau mu tabbatar da rayuwa mai inganaci ma kowa.

To saida shekaru biyu bayan furucinsa ciwon kanjamau ya kashe daya daga cikin 'ya'yansa.

A shekarar 1999 da ya cika shekar 85 da haihuwa
Nelson Mandela ya ce ya yi ritaya daga harkokin siyasa.
Amma ya cigaba da fafitikar kare hakin yara.

A kasar da ta yi shekara da shekaru tana fama da wariyar launi
ana ganin Nelson Mandela shugaba ne na gari.
Mutum ne wanda ya kawar da Afirka Ta Kudu daga tashin tashina
da kiyayya kana ya mayar da ita babbar kasa mai
zaman lafiya da fahimta.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG