Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahajjatan Najeriya na Shirin Komawa Gida


Mahajjatan hajjin bana sun kammala aikin wannan shekara, sun ma fara shirye-shiryen komawa gida, inda wadansu alhazan suka dukufa wajen sayen kayan tsaraba da maraba.

A wata hira da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz yayi da wani mahajjati mai suna Alhaji Dan Kawu Jagada daga Jihar Adamawa, wanda ya baiyana farin cikinsa da kammala aikin hajin bana, inda ma yace “na ji farin ciki, ba ni kadai ba, duk wani mai tunin arewacin Najeriya sa yakumace duk wani mutumin Arewacin Najeriya daya je Saudiyya, ya tsaya yayi addu’a Allah Ya kare mu”.

Akwai kuma wasu rahotanni ma dake cewa wasu mahajjatan sun sami hatsari a inda wani mahajjati ya rigamu gidan gaskiya, biyo bayan kade shi da mota tayi a Minna.

Babban likitan dake kula da mahajjatan Nageriya Dr. Ibrahim Kana ya kara tabbata da afkuwar hatsarin, ya kuma ce hukumomin Saudiya sun nuna yabonsu a bana ga goyon bayan da ‘yan Nageriya suka basu a harkokin Hajji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG