Farfesa Bello Bada, na jami’ar Usman Danfodiyo dake jihar Sokoto, ya bayyana cewa ziyarar da shugaba Muhammdu Buhari, ke gudanarwa a wasu daga cikin jihohin kudancin kasar, abu ne da ya dace domin hakan ya nuna hadinkai da rashin kyama ko wariyar ga wata kabila a fadin kasar.
A jiya Talata ne shugaba Buhari ya fara ziyarar kwanaki Uku a jihohi uku dake kudancin Najeriya, kuma jama’a sun fito kwansu da kwarkwata domin nuna farin cikin su da wannan ziyara da shugaban ke ci gaba da yi a yankin.
Da yake amsa tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka ya yi masa akan kalaman da jama’a ken a cewa shugaban ya Makara wajan kai ziyara a wannan yanki, Farfesa Bada, ya bayyana cewa ba’a Makara da ziyara cikin gida, kuma a cewarsa daya daga cikin alfanun da wannan ziyara zata haifar shine kara dankon zuminci tsakanin bangarorin kasar.
Daga karshe ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da suka kamata shugaba ya mayar da hankali akai sun hada da tabbatar da zaman lafiyar Najeriya, da kuma tattalin arzikin ta, domin a cewar sa da zarar an mayar da hankali kan wadannan muhimman abubuwa biyu, babu shakka za a sami nasarar ci gaban kasa mai dorewa.
Domin karin bayani, saurari rahoton Hassan Ummaru Tambuwal a nan.
Facebook Forum