Injiniya Suleiman Useni Adamu, ministan albarkatun ruwa na Najeriya y ace babu yadda za’a warware matsalar bushewar tafkin Chadi sai Najeriya ta nemi amincewar duniya a jawo ruwa zuwa tafkin.
Yace ya je wani taro a Birnin Paris a kasar Faransa dangane da batun. Zasu shirya babbar muhawara da kwararru domin a jawo ruwan zuwa tafkin.
Alhaji Bababo Abba dan masani Fika wanda ya taba zama babban sakataren raya kogin Kwara mai kasashe takwas dake da alaka da tafkin Chadi yace lokacin da tafkin Chadin yak e nan ba wuri ba ne na su kawai har masu yawon bude ido na zuwa wurin. Halin da tafkin ka ciki, Najeriya ita kadai ba zata iya gyarashi ba. Y ace wajibi ne ta samu amincewar duniya gaba daya a taron duniya da ake yi akan albarkatun ruwa saboda tafkin ya shafi kasashe bakwai.
Baicin batun tafkin Chadi, ministan y ace akwai wani sabon shirin yawaita Birnin Maiduguri da ruwa
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum