An cire Fahad al-Mowallad, daya daga jerin ‘yan wasan kasar Saudiyya da za su wakilce ta a gasar cin kofin duniya da za a fara a Qatar.
Hukumar kwallon kafar kasar ta Saudiyya ta cire Al-Mowallad ne saboda akwai shari’a da ake yi a kansa, kan samun burbushin Furesemide, wata kwaya da ke boye kwayoyin da ke kara kuzari.
A watan Fabrairu aka samu burbushin kwayar a jikin Al-Mowallad, amma duk da haka an saka shi a jerin ‘yan wasan.
An yanke masa hukuncin haramcin buga kwallo na tsawon wata 18.
Sai dai daga baya an janye shi a wani abu da kasar ta kira mataki na “kandagarki.”
Hukumar da ke yaki da tu’ammali da kwayoyi masu saka kuzari ta nemi a yanke masa hukuncin da ya fi wata 18.
Saudiyya na rukunin C a gasar ta cin kofin duniya, inda za ta fafata da Argentina, Poland da Mexico.