Da yake jawabi wa manema labaru a gidan gwamnati lokacin da wani kamfani ya kawowa 'yan gudun hijiran kudancin Kaduna tallafi, gwamna Nasiru El-Rufai yace kowane dan kasa nada hakkin ya zauna koina yake so saboda haka ba za'a bari a kori wani ba.
Yace kwanan nan zasu zauna su yi jawabi ga jiha domin su san tsare-tsaren da suka fito dasu na tabbatar da cewa an samu cigaba da zaman lafiya a jihar da adalci da kowa ba tare da nuna banbanci na addini ko kabilanci ba.
Inji gwamnan duk wanda ya zo jihar kuma yana son ya zauna hakkin gwamnati ne ta kare mutuncinsa kuma a tabbatar inda yake son ya zauna ya zaunan kuma babu wanda ya isa ya koreshi domin tsarin mulkin kasar Najeriya ya ba kowane dan kasa damar ya zauna duk inda yake so. Yace duk wanda yake ganin zai kori wani daga jihar Kaduna yayi kuskure kuma gwamnati sai ta ga bayanshi.
Saidai wasu kungiyoyin addini na ganin an riga an makara game da yadda za'a shawo kan rikici a jihar musamman a kudancin jihar.
Majalisar limamai da malamai ta jihar na ganin idan har ana son a shawo kan rikici a jihar to wajibi ne a kakkabe rahotannin baya a yi anfani dasu domin hukumta wadanda aka gano da laifi. Shaikh Abubakar Baban Time shugaban majalisar ya yiwa manema labarai karin haske game da matsayinsu.
Inji Shaikh Abubakar gazawar gwamnatocin baya na hukumta wadanda suke haddasa rigingimu dake kaiga kashe kashe ya sa har yanzu ake fama da tashin hankali. Yace a can baya kotun Okadigbo a shekarar 1992 ta samu Janar Lekwot da wasu mutane biyar da laifi ta kuma yanke masu hukumcin kisa amma ba'a aiwatar da hukumcin ba.
Saidai a wannan rikicin gwamnan jihar ya sake jaddada aniyarsa na hukumta duk wanda aka sameshi da hannu a rikicin. Amma jami'an tsaro zasu cigaba da ayyukansu na tabbatar cewa kowa an kare masa hakkinsa saboda ta haka ne kadai za'a sami zaman lafiya, inji gwamna El-Rufai.
Ga rahoron Isa Lawal Ikara da karin bayani.