Bayan shafe kusan shekaru biyu da takaita zuwa umrah da mahukuntar kasar saudiyya suka yi a wani mataki na rage yaduwar cutar korona da aka yi ta fama da shi a kasashe da dama a duniya, a bana dai kasar ta bude kofa ga maniyyata sama da miliyan guda a wannan wata ta Ramadan, duk da ka’idoji da aka shinfida an samu halartar mutane da dama.
Adadin da ake ganin ya zarce na sauran shekarun da suka gabata duk kuwa da tsadar kudin tafiya da kuma matakai da aka shinfida na kariya daga kamuwa da cutar korona.
Mazauna garin Madinatul Almunawara dake zama makwancin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW sun bayyana farin cikinsu game da bude kofa da aka yiwa baki a wannan karon wanda suka ce hakan ya basu dama da kuma karfin gwiwar yin ibada a cikin watan mai tarin falala.
A garin Makkah da ake sauke aikin umrah, yawan jama’a al’ummar musulmi ba’a iya cewa komai, duk sanyi duk zafi bai hana cikan mutane ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: