WASHINGTON D.C. —
A jamhuriyar Nijar shugabanin kungiyar kare hakkin manoma da makiyayan kasar wato Plate Forme Paysanne sun koka a game da yadda masu sayar da ciyawar dabobi ke barazanar batar da irin ciyawa a yankunan karkara, lamarin da ka iya haifar da koma baya ga sha’anin kiwo yayin da a daya bangare abin ke hanawa manoma samun takin gargajiya.
A cewar shugaban wannan kungiya Malam Djibo Bagna bunkasar kasuwancin ciyawar dabobi a manyan birane ne ya sa masu irin wannan sana’a, kakkabe dukkan albarkatun gonaki ba tare da la’akari da irin illolin da abin ka iya haddasawa ayyukan noma da kiwo ba.