WASHINGTON D.C. —
Kamar yadda watakila wasu daga cikin masu sauraron mu suka ji a makon da ya gabata, muna tattaunawa ne kan yadda annobar cutar korona bairos ta shafi harkokin noma a Najerya da kuma barazanar yunwa da al’umar kasar ke fuskanta. Muna kuma tattaunawa ne da Farfesa Mohammed Faguji Ishiyaku, Babban darekta na cibiyar binciken harkokin noma ta Samaru da ke Zaria da kuma Dr. Shu’aibu Madugu, darekta a majalisar bincike harkokin noma ta Najeriya wato ARCN da ke Abuja.
A cikin shirinmu na wannan makon, Farfesa Mohammed Faguji Ishiyaku, zai daura kan bayani da ya faro a makon da ya gabata, akan banbancin iruruwa da suka inganta da kuma wadanda ba’a inganta ba.