WASHINGTON D.C. —
Yayin da annobar cutar korona bairus ta bulla a larduna da kasashe kusan 220 a duniya, ta kuma shafi tattalin arzikin su da kuma harkokin yau da kullum.
A cikin shirinmu na wannan makon, za mu duba yadda wannan cuta ta shafi harkar noma a Najeriya da kuma barazanar yunwa da al’umar kasar ke fuskanta. Ba tare da bata lokaci ba zan mika ragamar shirin ga wakiliyarmu a Abuja Medina Dauda don jin yadda ta tattauna mana da bakin da ta gayyato mana.