A karshen wani taron da suka gudanar a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, kwararu da jami’an kare hakkin manoma da makiyaya sun kudiri aniyar tunkarar matsalar satar irin shukoki da na dabobi da ake fuskanta a ‘yan shekarun nan bayan la’akari da yadda wasu kamfanonin kasa da kasa ke manna tambarinsu a kan irin shuka duk kuwa da cewa abu ne da mazaunan karkara suka gada iyaye da kakanni.
Taron wanda ya sami halartar tawagogin kasashe 7 na CEDEAO da kasar Chadi, ya bada misalin yadda wasu ‘yan Senegal suka yi yunkurin mayar da irin albasar Galmi ta Nijar a matsayin mallakinsu, abin da ke zama wata barazana ga ci gaban ayyukan noma da kiwo a Nahiyar Afrika, kamar yadda za a ji sanarwar karshen taro daga bakin Diori Ibrahim na kungiyar Alternative.