Alluna 55 776 ne aka kafa a wani fili mai fadin hekta 27 a dajin Gorou Banda dake kwaryar birnin Yamai domin samar da wutar lantarki da hasken rana, tashar mai karfin megawatt 30 kwatankwacin bukatar mutane sama da 500000 za ta taimaka a cike gibin da ke haifar da karancin wuta a birnin Yamai sakamakon tangardar da ake fuskanta akai -akai a layin jigilar wuta da ke fito wa daga Birnin Kebbi kamar yadda shugaban kasa Mohamed Bazoum ya bayyana.
Kungiyar Tarayyar turai da kungiyar AFD ne suka hada guiwa da gwamnatin jamhuriyar Nijer don gina wannan tasha da ta lakume milliard kokuma billion 20 na cfa. babban wakilin kungiyar EU mai kula da hulda da kasashen waje sha’anin siyasa da tsaro Josep Borrell wanda ke ziyarar aiki a yanzu haka a Nijer ya fayyace matsayin wutar lantarki akan batun ci gaban tattalin arziki musamman ta hanyoyin da zamani ya zo da su sannan ya jaddada aniyar EU kan maganar ci gaba da bai wa wannan kasa tallafi.
Yace Turai na tare da ku za ta ci gaba da kasance wa da ku domin karfafa ayyukan da kuka sa gaba ta yadda yankin Sahel zai sami zaman lafiya al’umomi su yi rayuwa cikin jin dadi.
Nijar wace a yanzu haka ke gudanar da ayyukan hadin guiwa da nufin jona wuta a tsakananinta da kasashen Najeriya, jamhuriyar Benin, da Burkina Faso a karkashin wani tsarin kasashen yammacin Afrika a daya gefe, kasar ta kaddamar da shirin kafa tashoshin samar da wuta da hasken rana a jihohinta da dama.
Samar da wutar lantarki ta hanyar injin na kan gaban hanyoyin da ake amfani da su a yanzu haka a Jamhuriyar Nijar, a nan Yamai misali gwamnatin kasar a zamanin Issouhou Mahamadou ta kafa irin wannan tasha mai karfin megawatt 100 a matsayin matakin riga kafin tsinkewar layin wutar da ke zuwa daga birnin kebbi to sai dai masu fafutikar kare muhalli sun nuna rashin gamsuwa da wannan tsari mafari kenan hukumomi suka fara karkata wajen hanyoyin samar da makamashi mai tsafta a yayinda ake sa ran kaddamar da tashar makamashi ta kan Ruwan kogin Nijer bayan kammala ayyukan ginin madatsar kandaji dake jihar Tilabery.
Saurari rahoton cikin sauti: