A jamhuriyar Nijer ‘yar jaridar da hukumomi suka kulle a gidan yari a makon jiya bayan da dan shugaba Issouhou Mahamadou ya yi korafin ta yi masa kazafi ta gurfana a gaban alkali.
To sai dai tuni lauyoyinta suka fara yunkurin a basu belinta sakamakon yanayin rashin lafiyar da take fama da shi.
Wannan shine karon farko da ake gabatar da ‘yar jarida Samira Sabou a kotu mako 1 bayan garkame ta a kurkuku sakamakon karar ta da aka kai.
Mataimakin daraktan fadar shugaban kasa Maman sani Issouhou Mahamadou shi ne ya shigar da karar saboda a cewarsa ta yi masa kazafi bayan ta ruwaito a kafar facebook cewa yana da huldar kut da kut da daya daga cikin ‘yan kwangilar da ake zargi da handame dubban miliyoyin cfa a ma’aiktar tsaro.
Bayan kammala wannan zama Me Boudal Effred, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Samira ya bayyanawa manema labarai cewa yanayin rashin lafiyarta ne ya sa suka shigar da bukatar a bada belinta.
"Tana cikin mawuyacin hali, hatta shi kansa wanda ya yi kararta yana da masaniya akai saboda haka muke kira a yi aiki da hankali don kawo karshen wannan rikici maras di-digi," in ji lauyan.
Wata Cibiyar ‘yan jarida Maison de la Presse wacce ke bin diddigin wannan al’amari ta fara tuntubar bangaren mai korafi don ganin ya janye kararsa ta yadda za a warware abin cikin sulhu inji sakataren yada labaranta Souleymane Oumarou Brah.
‘Yar jarida Samira Sabou dai ita ce shugabar kungiyar masu fafutuka ta kafar Blog.
Saurari wannan rahoton a cikin sauti.
Facebook Forum