Shugabar kungiyar da ke kula harkokin makamashin nukiliya a Jamhuriyar Nijar wato HANEA, Zeinabou Mindaoudou Souley ta bayyana cewa sun hada wani rohoto da ya yi nazarin yiwuwar amfani da makamashin nukiliya wajen samar da wutar lantarki sannan aka aikawa hukumar ta IAEA domin ta tabbatar da sakamakon binciken.
Wannan shine matakin farko na tantance yiwuwar kaddamar da ayyukan samar da makamashin nukiliya a kasar Nijar da ta kasance daya daga cikin kasashen duniya da suka fi kowa arzikin karfen Uranium. Saboda haka wannan shirin zai .shafi yankin Afirka ta yamma gaba daya.
"Wutar da wannan shirin zai samar ya fi karfin Nijar ita kadai. Wutar domin kasashen yammacin Afirka ne," inji shugabar ta HANEA
Shugabar ta bayyana cewa, ana sa ran nan da shekaru 15, bukatar wutar zata karu a yankin yammacin afirka wanda dole sai da wannan makamashin.
Shugaban da ke wakiltar mataimakin shugaban hukumar IAEA, Anthony Stout ya bayyana cewa Jamhuriyar Nijar na da niyyar cimma wannan burin na wadatar wutar ganin yadda ta mayar da hankali wajen mutunta ka'idojin ayyukan kafa tashar makamashin nukiliya kuma hukumar ta yi alwashin tallafa mata.
Ana sa ran nan da shekarar 2030, wannan tashar za ta fara sarrafa makamashin domin samar da wutar lantarki. Hakan zai bunkasa ayyukan kamfanoni da masana'antu.
Saurari cikakken rohoton Suleiman Mumini Barma
Facebook Forum