An bude sallar Maradi Kwalliya a jamhuriyar Nijar a wani bangaren tunawa da samun jamhuriya shekaru 57 da suka gabata.
Kowace 18 ga watan Disamba kasar ke tunawa da samun zama jamhuriya wanda ya bata cikakken 'yanci daga mulkin mallaka da turawan Faransa suka yi mata.
Binkin ya kammala ne bisa jagorancin Firayim Ministan kasar Malam Birji Rafeni. Kimanin mutane dubu biyar suka halarci bikin na Maradi ciki ko har da wasu daga kasashen waje domin karfafa dankon zumunci.
Frayim Ministan ya yiwa Allah godiya da ya biya masu bukata. Yace sun shaida abun da aka yi a Maradi saboda ta yi kwalliyarta kuma kwalliyar ta biya kudin sabulu..
A wani gefen kuma Firayim Ministan ya jajintawa mutanen Diffa da rikicin Boko Haram ya daidaita tare da jami'an tsaro da yanzu suke bakin daga.
Ga karin bayani.