Kungiyar jama’atul-kitab-wa-sunna tare da hadin gwiwar ma’aikatar ministan cikin gidan a Jamhuriyar Nijar, sun shirya taron horo domin kara fahimtar da malamai hanyoyin kaucewa amfani da kalaman tayar da zaune tsaye ko na cutsa tsattsauran ra’ayi da mummunar akida a yayin gudanar da wa’azi ko hudubobi a masallatan Juma’a.
Taron na zuwa ne a wannan lokaci da masu ta da kayar baya ke fakewa da addini don jan ra’ayin jama’a.
Shugabanin makarantun Islamiya da limaman masallatan Juma’a da malaman da ke gabatar da wa’azi daga jihohi 8 na Nijar ne ke halartar wannan taro na tunatar wa akan mahimmancin zaman lafiya da kuma irin nauyin da ya rataya a wuyansu a matsayinsu na masu alhakin ganar da al’ummar musulmi kyawawan dabi’u da mutunta abokin zama.
Bayanai daga yankunan dake fama da matsalolin tsaro sun yi nuni da cewa kungiyoyin ta’addaci na fakewa da dalilan addini domin cusa wa jama’ar irin wadanan wurare tsatsauran ra’ayi da muguwar akida ta hanyar wa’azin da suke shiryawa.
Hakan ya sa ma’aikatar ministan cikin gidan Nijar ta yi na’am da wannan yunkuri na Kitab-Wa-Sunna saboda yadda abin zai taimaka a kaucewa fada wa tarkon masu tayar da kayar baya, in ji AbdoulSamad Yahaya, Darektan sashen da ke kula da addinai a ma’aikatar ministan cikin gida.
Ganin yadda sakonnin da suka shafi sha’anin addini kan yaduwa daga wannan kasa zuwa waccan musamman a wannan zamani na amfani da kafafen sada zumunta, ya sa kungiyar jamama’tul-kItab-Wa Sunna ta gayyaci limaman wasu kasashen Afrika domin su halarci wannan taro.
Kwanaki biyar za a shafe a wannan zama inda mashahuran malamai za su baje maudu’ai da dama game da batun zaman lafiya yayinda a daya bangare za a yi tunatar wa akan illolin da bambancin kabila da zaluncin shugabanin ka iya yi wa yunkurin zaman lafiya.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai: