Yau jumma’a ake sa ran wani alkali a Afirka ta kudu zai yanke hukunci kan bukatar beli da tsohon madugun mayakan sakai a Najeriya da ake zargi da hanu a mummunar harin boma bomai a birnin Abuja cikin wan nan wata.
Henry Okah,tsohon shugaban kungiyar MEND,ya musanta cewa yana da hanu a tagwayen hare haren da suka kashe mutane 12, a lokacin bikin zagayowar ranar da Najeriya ta sami ‘yancin kai.
Jiya Alhamis,masu gabatar sunce Okah ne kanwa uwar gami harin na ranar daya ga watan Okotoba,kuma ‘Yansanda sun gano rasit rasit na cinikin bindgigogi,da na’uorirjn harba gurneti.
An kama Okah ne a birnin Johannesburg bayan an kai harin.Ana tuhumarsa da makarkashiyar ta’addanci,da tada nakiyoyi. Hukumomi a Najeriya sun kama mutane tara dangane da wan nan batu.