Kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta sanar da bukatar dake a kwai ta gudanar da bincike da ka iya kaiwa ga tsige shugaba Donald Trump, bisa laifin neman kasar waje ta taimaka mishi don cin zaben 2020.
“Wannan matakin da shugaban ya dauka yau, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar,” a cewar Pelosi, shugaba Trump shi ke da hakkin duk laifin da yayi, don babu wanda yafi karfin doka.
Pelosi tayi wannan sanarwar ne a jiya Talata, bayan wata ganawa da tayi da wasu jagororin jam’iyyar a majalisar, ganin yadda ‘yan jam’iyyar Democrat ke kara saka hannu don a tsige shugaban.
A kwai wasu munanan aika-aika, amma babu wanda yayi kusanci da wannan, a cewar shugaban, haka ne, na hada baki. Me zaku yi akan hakan? Dan-majalisa Tom Malinowski ya shaidawa manema labarai.
Pelosi na zargin Trump da rashin mutunta alkawalin da ya dauka na zama shugaban kasa.
Facebook Forum