A yayin da a yau duniya ke bukin ranar fadakarwa game da kawo karshen cin zarafin mata, har yanzu ana bayyana cewa wannan matsala ta fi tsanani a kasashe masu tasowa irin na Afirka, Asiya da Latin Amurka, inda a bisa wasu dalilai na al'adu, ake tauye hakkin matan.
A hirar da wakilin VOA Hausa, Hassan Umar Tambuwal, yayi da wasu mata a garin Ibadan a yankin kudu maso yammacin Najeriya, kusan dukkansu sun bayyana rashin jin dadin yadda mazajensu ke musgunawa tare da take musu hakki.
Wata mace, ta bayyana wannan rana a zaman mai dadi kuma ta godiya ga Allah. Sai dai ta ce maza mayaudara ne, kuma ba su da alkawari, har ma ta ce idan aka ga namiji aka ga maciji, to gara a kashe namijin a bar macijin. Da wakilinmu ya tambaye ta ko idan ba maza din yaya zasu yi to, sai ta ce ai su na tare da Allah. Tana bayyana wannan ne kuwa a saboda irin ukubar da ta sha a hannun namiji.
Wata macen kuma ta ce ko da yake ba ta san da wannan rana ba, maza ba su da alkawari kamar mata, ba su fadar magana su cika. Da aka tambayeta a kan ko yaya zata ce game da ikirarin maza cewa sune suke ciyarwa su shayar da su, sannan ma har su kai su Makka ko su saya musu motoci, sai ta ce ai ba duk mazan ne masu haka ba, 'yan kalilan ne. ta ce akwai matan ma dake ciyar da maza da musu duk irin wadannan abubuwan idan aka ba su sukunin nema din.