Bilkisu Isyaku Ibahim, wata matashiya ce da ta fuskanci matsaloli da dama a lokacin da ta ke karatun ta na jami’a, kasancewar tana da lalura ta kafa wanda hakan ya sa ta fuskaci matsaloli a makarantar da ta ke zuwa, musamman zuwa ajujuwansu na can saman bene, wanda kusan hawa hudu ne kafin ta kai.
Bilkisu ta kara da cewa bata da matsalar ta hawa bene, ba kwas din da ta ke so ta karanta ba ne, amma hakan bai sanyaya mata gwiwa ba, ta kara da cewa baya ga haka kuma, zirga-zirga a cikin makarantar ma wani babban kalubale ne a gare ta.
Bilkisu ta ce bayan ta kamala karatun ta, ta dan samu ‘yar matsala inda sai da ta maimata aji daya a wani kwas na satistic na Education. Don haka bata fara neman aiki ba, kasancewar sai da ta yi wa kasa hidima, duk da cewar babban burin ta bai wuce ta karanci aikin jarida ba.
A maimakon ta yi jiran lokacin yiwa kasa hidima, wanda zai dau tsawon lokaci, sai ta ga hakan ya ba ta damar komawa karatu domin ta karanci abin da rai ke da muradi, watau aikin jarida. Daga nan ta shiga wata makaranta domin ta karanci aikin jarida amma na certificate.
Ta ce babban burinta a rayuwa shine ta zama cikakkiyar 'yar jarida da zata taimaki al’ummarta ta, kuma yi mata hidama yadda ya dace, shi ne abinda ta ke so ta cimma a rayuwarta.
Facebook Forum