Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar USAID Ta Amurka Ta Tallafawa Gwamnatin Bauchi da Littafai Miliyan Daya


Gwamnan Bauchi M. A. Abubakar a wurin kaddamar da sabon shirinda USAID ta shirya
Gwamnan Bauchi M. A. Abubakar a wurin kaddamar da sabon shirinda USAID ta shirya

Wani bincike da aka gudanar akan ilimin yara a jihohin Bauchi da Sokoto ya nuna cewa yara daga jihohin biyu nada matsalar koyon karatu dalili ke nan da ya sa aka bullo da sashen bada ilimi mai inganci da zai taimakawa yaran iya karatu da rubutu a lokaci guda.

Malam Ahmed Umar Sokoto baturen koyon karatu na Northern Education Initiative a jihar Bauchi ya shaidawa Muryar Amurka yadda za'a gudanar da sabon tsarin koyaswar.

Yace sabon tsarin zai taimakawa yara su iya karatu da Hausa da Turanci yayinda suka kai aji ukku a makarantar firamare. Tsarin ya kunshi matakai ukku da ya shafi abun da malami zai yi, sai kuma abun da yara zasu yi da abun da kowane yaro zai yi da kansa. Baicin matakan ukku akwai kuma auna fahimtar yara da za'a dinga yi mako mako da na wata wata.

Shirin Inganta Ilimi da USAID ta taimaka aka samu
Shirin Inganta Ilimi da USAID ta taimaka aka samu

Gwamnan jihar Barrister M.A. Abubakar yace an samar da kudi kashi talatin cikin dari na ilimi kamar yadda yake a kasafin kudin jihar. Ya gargadi 'yan makaranta da daliban sakandare cewa su tashi su rungumi shirin USAID na inganta ilimi a jihar.

Shugaban ilimi na daya Yahaya Ibrahim Yero yayi karin haske kan shirin inda yace akwai horaswan da za'a yiwa malamai saboda su aiwatar da aikinsu yadda ya kamata kafin a rabawa dalibai littafan karatu da zasu yi anfani dasu.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG