Kungiyoyin mata masu kare muhalli sun sha alwashin kai karar gwamnatin jahar Delta bisa laifukan gurbacewar muhalli sakamakon dagwalon man fetur, wanda ke haifar da rashin lafiya da ingantacciyar rayuwar al'ummar jihar.
Kungiyoyin sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a karshen mako a Lagos inda wata basarakiya ta jahar mai suna Lori Ogbwebu ta jagoranta, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saka baki domin ganin cewa an kawo karshen gurbacewar a yankin Naija Delta.
Koda yake kungiyar ta yaba da matakin da shugababn kasa Muhammadu Buhari ya dauka na amincewa da kwashe dagwalon man fetur a yankin Ogoni na jahar Rivers, ta ce akwai bukatar shugaban ya sa ido domin ganin an dauki irin wannan mataki a sauran wuraren.
Ta kara da cewa jama'ar yankin ba su da ilimi, basu da makarantu, basu da abinci, basu da ruwan sha mai kyau kuma lallai suna cikin wahala matuka, suna bukatar taimakon gwamnati.
Daga karshe ta kara jaddada baynin da ta yi da farko na bada tabbacin kai karar gwamnatin kotu, kuma ta ce karar gwamnati ba itace karshen matsalar kawai ba domin kuwa gwamnati na iya yin ko oho da lamarin, amma sun mika kukan su ga gwamnatin tarayya da ta duba ta kuma tausaya masu.