Bayan rufe layikan sadarwar kamafanonin MTN, Glo, Airtel da dai sauransu, al’ummar Najeriya na kokawa a kan yadda wannan matakin ke ci gaba da jawo musu asara, yayin da kuma wasu masana ke cewa a cikin lallami ya kamata a bi 'yan kasa don hade layikansu da lambar shaidar dan kasa, wasu kuma na ganin dole a fifita ‘yancin ‘yan kasa a kan komai.
Masana dai sun ce akwai yiyuwar matakin na hukumar sadarwa ta Najeriya wato NCC ya kai ga rufe kimanin layin sadarwa sama da miliyan 11 biyo bayan cikar wa'adin ranar 28 ga Fabrairu na haɗa lambar shaidar zama dan kasa wato NIN da Lambobin wayoyin tarho.
Kamfanonin sadarwar da ke kasuwancinsu a Najeriya dai na bin umarnin hukumar NCC ne ganin yadda daraktan hulda da jama’a na NCC, ya sake shaida wa manema labarai cewa wa’adin hukumar na ranar 28 ga Fabrairun shekarar 2024, ya cika, kuma ba gudu ba ja da baya kan matakin, yana mai cewa masu amfani da layikan wayar salula da su tuntubi kamfanonin sadarwarsu don hade SIM cards dinsu da lambar NINs don sadarwa.
Tuni dai wasu ‘yan Najeriya ke ta kokawa a kan yadda matakin NCC da kamfanonin sadarwar kasar suka aiwatar ya jawo musu asara mai tarin yawa.
Wani Mazaunin jihar Osun dake yammacin Najeriya, Abdulganiy Abdulrahman, ya ce matakin kamfanin MTN ya jawo masa asara yana mai mika bukatar a bude masa layinsa.
A cewar wani mazaunin jihar Sakkwato, Abdulrahman Salihu Abba, matakin kamfanonin sadarwar ya gurgunta masa al’amurran kasuwanci abun da aka dauki tsawon lokaci bai fuskanta ba a baya.
A wani bangare kuma, kwararre a fannin sadarwa kuma tsohon kwamishinan yada labaran jihar Adamawa, Alhaji Ahmad Sajoh ya ce kamata ya yi kamfanonin sadarwa da gwamnati su bi ‘yan Najeriya da lalama, a fahimtar da su mahimmancin hade layikan sadarwarsu da lambar NIN ba wai amfani da iko ba.
A yayin da ake cece-kuce a kan cewa akwai hukuncin kotu da ya hana hukumar NCC aiwatar da matakin rufe layikan sadarwar wadanada ba su hade nasu da lambar NIN ba, masanin shari’a Barrister Mainasara Kogo ya ce, ‘yan kasa na da ‘yanci kamar yadda hukumar NCC ma na da yancin daukar mataki yana mai cewa a yi la’akari da sashe na 14 sakin sashe na 1 na tsarin mulkin Najeriya wanda ya ce domin jama’a ne ake neman ‘yanci.
Idan ana iya tunawa, a ranar 16 ga watan Disamban shekarar 2020 ne gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin a haɗa layikan sadarwa wato SIM card da lambar shaidar zama dan kasa wato NIN tsarin da aka fitar da nufin magance matsalar rashin tsaro a kasar ta hanyar taimaka wa hukumomi wajen zakulo ‘yan fashi da ‘yan ta’adda.
Bayanai daga shafin intanet na hukumar NCC sun yi nuni da cewa akwai layikan wayar hannu miliyan 224 da dubu 700 da ke aiki a Najeriya saidai kuma hukumar kula da rijistar shaidar dan kasa ta NIMC ta ce ya zuwa yanzu ta yi bayar da lambar NIN miliyan 104.
Saurari rahoton Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna