Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Girka 'Yan Sanda A Cibiyoyin Sadarwa


'Yan sandan Najeriya su na yin sintiri a garin Kaduna a arewacin kasar
'Yan sandan Najeriya su na yin sintiri a garin Kaduna a arewacin kasar

Kungiyar nan da ake kira Boko Haram ta dauki alhakin kai hare-hare kan cibiyoyin na wayoyin salula tana cewa su na taimakawa jami'an tsaron kasar

Sufeto-janar na ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umurnin sanya idanu dare da rana a kan dukkan cibiyoyin sadarwa ta wayar tarho a kasar, a bayan da aka kai hare-haren da suka lalata eriya ta wayoyin salula a wasu sassan arewacin kasar.

Kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram ta dauki alhakin wadannan hare-hare a jiya alhamis, tana mai fadin cewa kamfanonin na wayoyin salula su na taimakawa jami’an tsaro wajen bin sawu da kama ‘ya’yan kungiyar, a bisa dukkan alamu a lokutan da suka kunna wayoyinsu ko suke amfani da su.

A cikin wata sanarwar da aka ce kungiyar ce ta bayar, ta ce zata ci gaba da kai wadannan hare-hare har sai kamfanonin sun daina taimakawa gwamnati wajen yakarsu.

Wadannan hare-hare sun sa sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar, ya umurci kwamandojin ‘yan sanda a jihohi da kananan hukumomi da su kafa wasu bataliyoyi na musamman domin kare cibiyoyin sadarwar wayar tarho. Ya roki jama’a da su sanar da ‘yan sanda idan sun ga wani abu ba daidai ba yana gudana.

Har ila yau a jiya alhamisar, kungiyar ta Boko Haram ta yi barazanar kai farmaki a kan ma’aikata da wakilan gidan rediyon nan na Muryar Amurka, tana mai zargin VOA da laifin daukar matakan cutar da addini. Wannan sashe na Hausa yana watsa shirye-shiryensa ne zuwa Najeriya.

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyar take yin barazana ga wannan gidan rediyo da ma’aikatansa.
XS
SM
MD
LG