Kakakin shugaban, Reuben Abati, yace ana tattaunawar “bayan fage” domin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman a yankin arewacin Najeriya inda tashin hankalin ya fi tsanani.
Abati ya fadawa ‘yan jarida jiya lahadi a Abuja cewa gwamnati tana son ta fahimci irin koke-koken da kungiyar ke da su domin ta iya kawo karshen wannan tashin hankali. Amma kuma yace gwamnati zata dora ma duk wanda ya keta doka alhakin hakan.
Wannan furuci na Reuben Abati, shi ne karon farko da wani jami’in gwamnati ya fito fili yace Najeriya tana tattaunawar neman yin sulhu da kungiyar Boko Haram.
A baya cikin wannan watan ne wani mutumin dake ikirarin cewa shi mai magana da yawun kungiyar ne ya fadawa Muryar Amurka cewa su na tattaunawa da gwamnati a saboda rokon da jama’a ke yi na ganin an yi sulhu.