Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NANS Ta Fasa Zanga-Zangar 12 Ga Watan Yuni


Daliban jami'o'in Najeriya yayin wata zanga zanga da suka yi a Abuja a 2018 (Twitter/@NANSNIG)
Daliban jami'o'in Najeriya yayin wata zanga zanga da suka yi a Abuja a 2018 (Twitter/@NANSNIG)

Kungiyar Daliban Najeriya – NANS, ta jingine gudanar da gagarumar zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranar Assabar, 12 ga watan Yuni, a yayin da kuma ta nisanta kan ta da fafutukar kin jinin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kungiyar ta Daliban Najeriya ta shirya gudanar da zanga-zanga a ranar ta bikin dimokaradiyya ta Najeriya, wato 12 ga watan Yuni, domin nuna damuwa akan yanayin da kasa ta ke ciki na tabarbarewa tsaro, da kuma musamman yawaitar satar daliban makarantu da ‘yan bindiga ke yi.

To sai dai wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Sunday Asefon ya fitar da safiyar Juma’a, jajibirin ranar gudanar da zanga-zangar, ta ce kungiyar ta sauya tunani, haka kuma ta jingine gudanar da zanga-zangar.

Sanarwar ta ce an dau wannan matakin na dakatar da yin zanga-zangar ne “saboda kiyaye lafiyar masu zanga-zangar, da kuma fargabar cewa ‘yan siyasa na iya karkatar da akalar zanga-zangar zuwa ta su manufa ta siyasa.”

Asefon ya ce an shirya zanga-zangar ne ta kasance ta lumana domin nuna damuwa da halin da kasa take ciki, to amma tuni wasu ‘yan siyasa da ke da wasu manufofi na daban sun soma shirin karbe akalar zanga-zangar, domin cimma wasu maufofi na kashin kan su.

Tuni dai da wasu kungiyoyi a fadin kasar suka amsa gayyatar farko ta kungiyar na shiga zanga-zangar, inda a wasu yankunan ma har suka kara manufofin zanga-zangar da suka hada da kalubalantar matakin gwamnati na dakatar da Tuwita a Najeriya, fafutukar ballewa daga kasar da kuma fafutukar ganin bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar daliban Najeriya, NANS, Sunday Asefon, (Facebook/Sunday Asefon)
Shugaban kungiyar daliban Najeriya, NANS, Sunday Asefon, (Facebook/Sunday Asefon)

Sai dai shugaban kungiyar ta NANS ya ce kunkiyar ta dalibai ba ta da alaka da wata siyasa, ko fafutukar ballewar ko wane yanki daga Najeriya, ko kuma fafutukar kin jinin shugaba Buhari.

Ya ce “wannan ne dalilin da ya sa bayan tattaunawa da dukan shugabannin kungiyar, muka yanke shawarar dage gudanar da zanga-zangar, domin kiyaye lafiyar membobin mu, da kuma fargabar juya alkiblar zanga-zangar zuwa wata manufa ta siyasa.”

“Mun shirya zanga-zangar ne domin samun inganta sha’anin tsaro da inganta jin dadin rayuwar dalibanmu, don haka ba zai yiwu kuma mu jefa rayukan daliban cikin hatsari ba ta hanyar zanga-zangar,” in ji Asefon.

To sai dai kuma ya ce zanga-zangar tana nan ba soke ta aka yi gaba daya ba, amma za’a sanar da sabon lokaci na gudanar da ita a nan gaba kadan.

XS
SM
MD
LG