Shugaban kwastam Umaru Yusuf, ya tabbatar da cewa hukumar ta kama manya-manyan buhunan tabar wiwi har 43, wanda hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi suka kiyasta cewa kudinsu ya kai Naira Miliyan 250.
A cewar shugaban kwastam din kayan dai sun fito ne daga kasar Ghana, domin cikin wannan shekarar hukumar kwastam ta sha kama ire-iren wannan kayayyaki har sau biyar, wanda kudinsu yakai Naira Miliyan 700.
Game da shinkafar roba da akace an kama a gundumar hukumar kwastam dake Ikeja Lagos, yanzu haka dai an mika shinkafar ga hukumar NAFDAC domin tantancewa da tabbatar da gaskiyar lamarin.
Hukumar kwastam dai ta bukaci goyon bayan jama’a wajen yaki da ‘yan fasa kwauri a ko ina a fadin Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.