Majalisar Dokokin Najeriya ta samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan bukatar gyara ginin Majalisar, wacce a halin yanzu an kwashi sama da shekaru ashirin ana amfani da shi ba tare da gyara ba.
Wanan kwaskwarima ana sa ran za ta lakume kudi har Naira Biliyan 37 daga cikin kasafin shekara 2020 na babban birnin Tarrayya Abuja.
Shugaban masu rinjaye Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi, shi ne ya yi bayanin irin gyare-gyaren da za a yi, musamman ta wasu na'urorin magana wadanda ke amfani da wuta ba sa aiki, saboda an dade ba a gyara su ba, kuma ya ce igiyoyin wutar suna iya tada gobara.
Amma wannan bayani ne da ya ba kwararre a fannin tattalin arziki Abubakar Ali haushi, inda ya ce maimakon gyara ginin Majalisa, ya kamata yan Majalisar su zuba wadanan kudade a fannonin ilimi, da kiwon lafiya domin a samar wa talaka saukin rayuwa.
Shi ma masanin harkokin siyasa da zamantakewa Abubakar Aliyu Umar, ya ce wannan hanya ce ta almubazzaranci da kudaden kasa, inda ya koka cewa sai an ci bashi ake aiwatar da kasafin kudi, amma kuma ana kashe su ta hanyar kawa maimakon yi wa talaka aiki.
Abin jira a gani shi ne irin tasirin da gyara Majalisar za ta yi wa al'umma wajen samun dokoki da za su sauya rayuwar su.
Ga rohoto cikin sauti.
Facebook Forum