Hukumar raya kasashe masu tasowa ta kasar Burtanita DFID karkashin shirin ta na bunkasa kiwon lafiyar mata wato Women for Health, ta kafa cibiyar yayin da cibiyar bincike da nazarin jinsin bil’adama ta Jami’ar Bayero zata kula da ayyukan cibiyar.
Dr Fatima Ladan Daraktar shirin bunkasa kiwon lafiyar mata a Najeriya wato Women for Health, tace akwai babbar matsala a jihohin ta rashin ma’aikatan kiwon lafiya mata kuma dalilin kenan suke wannan aiki, sai dai tace, har izuwa yanzu matsalolin na karuwa. Tace dan haka ne suka yi hadin gwiwa da jami’ar domin ta cigaba da aikin.
Yanzu haka dai gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyar cin gajiyar ayyukan wannan sabuwar cibiyar horar da mata dabarun kiwon lafiya. Dr Tijjani Hussaini sakataren zartarwa na hukumar lafiya a matakin farko ta jihar, ya kuma ce gwamnatin Kano zata tura ma’aikatan lafiyarta domin karo ilimi.
A bana ne dai wa’adin shirin bunkasa kiwon lafiyar mata a Najeriya na hukumar raya kasashe ta kasar Burtaniya wato DFID ke karewa, bayan gudanar da ayyuka na tsawon shekaru bakwai a jihohin Kano, Jigawa, Zamfara, Katsina Yobe da kuma Borno.
Ga Karin bayani da wakilin mu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana:
Facebook Forum