Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Matsalar Da Kudin Lira Na Turkiyya Ke Fuskanta Za Ta Iya Shafar Naira?


Wata mata a Turkiya ta na musayar Lirar Turkiya da dalar Amurka kafin dalar da kara tsada
Wata mata a Turkiya ta na musayar Lirar Turkiya da dalar Amurka kafin dalar da kara tsada

Masana tattalin arziki na ganin takaddamar kasuwanci da ta kunno kai tsakanin Turkiya da Amurka ka iya yin tasiri a kasashen Afirka, musamman a Nigeria inda kawo yanzu Nigeria na sayen kayan da kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 1.2 a shekara.

Kwararru a fannin tattalin arziki sun yi hasashen cewa takaddamar da ke tsakanin Amurka da Turkiyya, wacce ta sa darajar Lira ta fadi ka iya shafar wasu kasashen Afirka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lura da yadda lamarin ke tafiya kasar na iya fadawa cikin matsalar tattalin arziki nan da shekara daya.

Halin da Turkiya ta tsinci kanta ciki ya sa kungiyar Tarayyar Turai na neman yadda za ta taimakawa Shugaba Recep Tayyib Erdogan.

Rikicin Turkiyan ya riga ya jefa wasu kasuwannin nahiyar Turai dama takardar kudin Nigeria, wato Naira cikin wani halin matsi a makonni biyun da suka gabata bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya kakabawa Turkiya takunkumi.

Matakin takunkumin ya sa darajar Lira ta ragu da kashi 40 cikin 100.

Akan aluminium da ke shigowa daga Turkiya, Amurka ta kara kaso 20 kan kudin fiton da ake biya. ta kuma kara kaso 50 kan karafa.

Ita Turkiya kuma sai ta mayar da martani inda ta aza kaso 140 akan jiya dake shigowa daga Amurka, kaso 60 akan taba da kaso 120 akan motoci. Ta na kuma shirin kara haraji akan wasu kayayyakin da suka hada da kayan shafawa, shinkafa da gawayi.

Masana a Nigeria na ganin wannan takaddamar ka iya tarwatsa tattalin arzikin kasashen Afrirka musamman kasashen da ke da dangantakar kasuwanci da Turkiya.

Misali kasuwancin da ke tsakanin Nigeria da Turkiya ya kai na dalar Amurka biliyan 1.2. Babu mamaki a samu hauhawan farashin kayan da ke shigowa daga Turkiya din a cewar jaridar ta Daily Trust.

Haka kuma farashin dalar Amurka yo soma hawa inji wani masanin tattalin arziki David Akwu na Jami'ar Nigeria da ke Nsukka.

A cewar shi, ya kamata mahukuntan Nigeria su yi takatsantsan da abubuwan da ke faruwa tsakanin Amurka da Turkiya, tsakanin Amurka da China lura da cewa kasashe ne da kasar ke kasuwanci da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG