Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutun-Mutumi "Robot" Na Iya Inganta Rayuwar Yara Nakasassu!


Jebo, social robot on display at the Robot Ranch.
Jebo, social robot on display at the Robot Ranch.

Wani bincike da aka gudanar da ya bayyanar da cewar, mafi akasarin mutun-mutumi “Robot” a turance, da ake kirkira a duniya, akan yi amfani da su ne a mafi yawancin ma’aikatu, ko kamfanonin kera motoci, tuka mota, shaguna don dukar kaya da dai makamantan su.

Baya ga haka ba’a amfani da wannan mutun-mutumin a wasu hanyoyi na rayuwar dan’adam. Amma wannan binciken ya bayyanar da cewar, idan za’a yi amfani da robot wajen taimakama yara masu nakasu, lallai da za’a ci ribar kirkirar shi fiye da yadda ake yi a yanzu.

Sabon mutun-mutumi da aka kirkira na farko a duniya don gwada yadda zai taimaka ma yara, mai suna “Leka” yana amfani da na’urar bulutut don hada shi da waya, yara masu nakasu kan iya amfani da shi don ya dinga debe musu kewa, da kuma basu damar kara fahimtar karatu da abubuwa a rayuwa. Yara da ke fama da matsalar bunkasar kwakwalwa, da wasu sassan jiki kan iya amfani da robot don motsa jiki da samun wayewa da zatayi dai-dai da abokan haihuwar su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG