A shirinmu na nishadi a yau dandalin VOA yana jihar Kaduna ne, inda kwanakin baya ne kafar sadarwa ta Facebook da WhatsApp suka dau batun rasuwar jarumi Rabiu Rikadawa da cewar ya mutu.
Labari dai ya je ga jarumin, ya kuma musanta hakan, inda ya ce wannan mutuwa ta sa, ta auku ne a wani shirin fim da suke gabatarwa – wanda ya yadu a gari aka dauka da gaske ne.
Jarumin ya ce karya ce kawai wani ne ya samu hoton mutuwarsa a wani fim da suke yi mai suna Raliya, wanda ya saka a kafar sadarwa na cewar Rabiu Rikadawa ya mutu, batun dai ya jefa masoyansa cikin damuwa da dimuwa.
Rikadawa ya ce wannan kafa ta saba yada labarin jita-jita musamman ma idan aka yi rashin sa’a ga wanda ya ke duba labarin, ya ce labarin ya janyo damuwa da tashin hankali baya ga daukar alhaki da aka yi ga masoyansa.
Sannan ya kuma kara da cewa, hakan ya sanya shi cikin takura da damuwa wanda ya ke cewa idan ma wasa ne wannan ya wuce gona da iri domin ya sanya mutane suna Allah wadai da wannan matsala da aka haifar.
Shugaban cibiyar bincike da wayar da kan al’umma akan yadda ake amfani da kafofin yanar gizo a jihar Kano da ke Najeriya, Bashir Sharfadi, ya yi mana fashin baki na yadda za’a tantance sahihanci labarai.
Sharfadi ya ce daman mutane na daukar labarai daga kafofin sadarwa ba tare da sun lura da sahihanci wannan labari ba, kuma ba tare da sun yi la’akkari da cewar akwai hanyoyi da akan iya hada hotuna ko faifan bidiyo a matsayin wani labari da zai ja hankalin mutane.
Masanin ya ce akwai wata hanya wacce ake cewa ‘Google Reverse Image’ da za ta tantance sahihancin wannan hoto ko bidiyo, a matsayin wata hanya ta tantance labarai.
Facebook Forum