Akalla yara hudu na daga cikin wadanda rugujewar ta rutsa da su a Kiteezi ranar Juma’a, kamar yadda ‘yan sanda suka shaida wa manema labarai.
Ana kyautata zaton ruwan sama ne ya janyo rugujewar wurin sharar. Ba a fayyace cikakkun bayanai game da abin da ya faru ba, amma hukumar birnin ta ce an samu "raguwar tsarin karfin wurin da dinbin shara."
Irene Nakasiita, mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross ta Uganda, ta ce babu wani sauran fatan ceto wasu mutane da ransu.
Ba a dai bayyana adadin mutanen da ba a ji duriyarsu ba. Wurin zubar da shara na Kiteezi wani babban juji ne a wani yanki mai fama da talauci wanda ke karbar daruruwan motocin dakon shara a kullum. Hukumar birnin ta yi niyyar soke shi tun bayan ayyana shi shekaru cikakku da suka gabata.
-AP
Dandalin Mu Tattauna