Hukumomin a Chadi sun baza dakaru a sassan kasar musamman a N’djamena, babban birnin kasar, a wani mataki na kwantar da duk wata tarzoma da ka iya tashi, bayan da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 6 ga watan Mayu.
A wani abu na bazata, hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon a daren Alhamis inda Shugaba mulkin sojin kasar Janar Mahamat Idriss Deby ya lashe zaben da kashi 61 cikin 100 na kuri’un da aka kada.
Sai dai babban abokin hamayyarsa Succes Masra na ikirarin shi ya lashe zaben da kashi 73 cikin 100 na kuri’un da aka kada.
Da safiyar Juma’a al’umar birnin ta N’djamena ta wayi gari da jin karar harbe-harben bindiga.
Wani mazaunin birnin mai suna Oumar ya ce mai yiwuwa gwamnatin ta Chadi ce ta ba da umarnin yin harbi a wani mataki na tsorata masu adawa da sakamakon zaben.
An dai fitar da sakamakon zaben mako guda gabanin wa’adin da aka yi tsammanin za a sanar da shi.
Alkaluman zaben sun nuna cewa Deby Itno ya samu kashi 61 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin da Masra ya samu kashi 18.5 cikin 100.
Tun gabanin sakin sakamakon Masra ya yi zargin cewa an tafka magudi.
Zaben na Chadi ya wakana ne bayan shekaru uku da kasar ta zauna karkashin mulkin soji.
Tun da farko dama masu fashin baki sun yi hasashen cewa Shugaba Deby Itno ne ake sa ran zai lashe zaben wanda ‘yan takara goma suka fafata ciki har da mace daya.
A shekarar 2021 Shugaba Itno ya karbi raganar mulkin kasar daga hannun mahaifinsa da aka kashe a fagen daga, wanda ya kwashe shekru sama da 30 yana mulki.
Hukumar zaben kasar ta ce mutum miliyan 8.2 ne aka yi rijista don kada kuri’arsu a wannan zabe wanda aka tura dakarun kasar sama da dubu 26 su kare rumfunan zabe.
Dandalin Mu Tattauna