Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Na Ci gaba Da Mutuwa A Kokarin Tsallaka Ruwa Don Isa Ingila Daga Faransa


Wani kwalekwale dauke da bakin haure
Wani kwalekwale dauke da bakin haure

Bakin haure sama da 26,600 ne suka tsallaka ruwa tsakanin Faransa da Ingila akan kananan jiragen ruwa a shekarar 2024, kamar yadda ofishin ma’aikatar cikin gida na Inglila ya sanar.

Adadin bakin haure 973 ne suka tsallaka ta ruwan da ke tsakanin Faransa da Birtaniya ta kananan kwalekwale, a rana guda da mutane 4 suka mutu yayin da suke kokarin shiga Birtaniya daga Faransa, kamar yadda alkaluman ofishin ma’aikatar cikin gida ta nuna a ranar Lahadi.

Adadin shi ne mafi girma a rana guda na bakin hauren da suka nutsewa garin yin irin wannan tafiya a bana, da ya zarta na baya, na adadin mutum 882 da aka samu a ran 18 ga watan Yuni.

A rana guda ne kuma aka samu wani yaro dan shekaru 2 da manya su 3 da suka rasa ransu, sakamakon matsalar da kananan jiragen ruwan da ya dauko mutane sama da kima ya samu, a yayin tafiyar mai hadari ta kokarin tsallakawa ta ruwa, da dubban mutane ke yi a duk shekara.

Hadarin shi ya kai yawan bakin hauren da suka rasa ransu a kokarin tsallaka ruwan a bana zuwa 51, cewar Jacques Billant, babban jami’in yankin Pas-de-Calais na Faransa.

Bakin haure sama da 26,600 ne suka tsallaka ruwa tsakanin Faransa da Ingila akan kananan jiragen ruwa a shekarar 2024, kamar yadda ofishin ma’aikatar cikin gida na Inglila ya sanar.

Hukumomi da masu gabatar da kara sun ce, mai yiwuwa mace-macen na karshen mako sun auku ne sakamakon cunkoson jama’a a kananan jiragen ruwan.

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya Yvette Cooper ta fada a ranar Asabar cewa, akwai yiwuwar mutanen da suka mutu a ruwan ya fi adadin da aka sani.

Yvette ta rubuta a kafar sadarwar zamani ta X cewa, kungiyoyin masu aikata laifin safarar mutane na ci gaba da shirya irin wadannan tafiye-tafiye ta kananan jiragen ruwa masu hadarin gaske.

Ta ce "irin wadannan kungiyoyin ba su damu da ko mutane su mutu ko su rayu ba- wannan muguwar sana’a ce da ake yi da rayukan mutane"

Sabuwar gwamnatin Labor ta Keir Starmer na fama da radadin rage masu tsallaka ruwan ta kananan jiragen ruwa zuwa cikin kasar, wani lamari da ya zama babban batu a babban zaben watan Yulin da ya gabata.

Gwamnati dai ta sha nanata kudurinta na ganin ta murkushe wadannan kungiyoyin miyagu na masu safarar mutane da ke shirya irin wadannan tafiye-tafiye na sayar da rai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG