Musulami sun shiga bukukuwan sallar Eid- al Adha, ko kuma babbar salla a sassan duniya, bayan da aka kammala Hawan Arfa a jiya Asabar a kasa mai tsari, inda mahajjata daga sassan duniya suka hallara domin sauke farali.
A Najeriya, shagulgulan sun kankama a sassan kamar yadda rahotanni ke nunawa, inda jama’a maza, mata da yara kanana suka dunguma zuwa masallatai domin gudanar da sallar idi.
A wani sakon taya Musulman Najeriya murnar wannan rana, shugaba Muhammadu Buhari, ya yi kira ga al’umar musulman kasar, da su rika nuna halayen da sauran jama’a za su rika dora koyarwar addinin Islama akan mizani mai kyau.
A can Jamhuriyar Nijar ma, rahotanni sun yi nuni da cewa, an fara gudanar da shagulgula lami lafiya, inda jama’a suka yi tururuwar zuwa masallatai da safiyar yau Lahadi, kafin daga bisani a gudanar da ayyukan layya.
A Kamaru da Ghana ma haka labarin yake, inda aka bude bukuwan sallar da zuwa masallatan idi da kuma cin abinci iri-iri, inda daga bisani aka yi ayyukan layya da kuma kai ziyara ga ‘yan uwa da abokan arziki.
Yayin da aka fara bukuwan sallar a sassan duniya, a yau Lahadi mahajjata suka yi jifan shedan a kasa mai tsarki, daya daga cikin rukunan aikin hajji.
Sama da alhazai miliyan biyu ne suka halarci aikin hajjin na bana, wanda ake yi a duk shekara, ake kuma kwashe kwanaki biyar ana yi.
Hukumomi a Riyadh, babban birni Makka, sun yi amfani da dubun dubatar jami’an tsaro, wadanda suka rika taimakawa alhazai, domin a kaucewa matsalar turereniyar da ta auku a shekarar 2015, inda mahajjata 2,300 suka rasa rayukansu,.
Abokin aikinmu Yusuf Aliyu Harande, wanda shi ma yake gudanar da aikin hajjin, ya tabbatar da irin matakan da aka dauka.
“Jami’an tsaron suna ta kai-komo babu kakkautawa, kowanne wuri aka bi za a gansu suna kai dauki.” In ji Harande.
Shi dai aikin Hajji, daya ne daga cikin shikashikan Musulunci guda biyar, wanda ake bukatar duk Musulmin da ke da hali da koshin lafiya ya cika shi, ko da sau daya ne a rayuwarsa.