Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmai  a Fagen Siyasar Amurka


Lokacin da Musulmi su ke zanga zangar nuna kyamar kalaman dan takarar jam'iyar Republican akan Donald Trump na nuna wariya ga Musulmi
Lokacin da Musulmi su ke zanga zangar nuna kyamar kalaman dan takarar jam'iyar Republican akan Donald Trump na nuna wariya ga Musulmi

Sarwat Husain ta san cewa hijabin da ta kan saka, a wasu lokuta ya kan ja hankulan jama'a a jihar ta Texas. Amma kallon da wani mutum ya mata, yayin da ta ke cikin jirgi akan hanyarta ta zuwa birnin Orlondo na jihar Florida, ya fita daban

“Bayan da jirginmu ya tashi, sai mutumin ya ce min, da a ce wannan tagar kofa ce, da na wurga ki waje, sai na cika da mamaki.” In ji Sarwat.

“Sai na kalle shi na ce, ni kuwa da na janyo ka mun fada tare.”

Wannan amsa da ta ba shi sai ta dan kwantar da hankula a cikin jirgin, sai kuma ya yi dariya ya ce “Ah! Lallai ke mai barkwanci ce, sai na kalle shi na ce wannan ba abinda dariya ba ne ko kadan.”

Wannan lamari dai ya faru ne kusan makwanni uku da suka gabata.

Abinda dai da abokin zaman ta bai sani shi ne, Sarwat na kan hanyar ta ne ta zuwa Orlondo domin halartar wani taro da kwamitin jam’iyyar Democrat ya shirya, wanda zai tsara babban taron jam’iyyar ta Democrat.

Sarwat ita ce shugabar da ta kirkiro reshen majalisar zumuntar Musulmi a birnin San Antonio da ake kira (CAIR) a takaice.

Tana kuma daya daga cikin wadanda suka kafa reshen kungiyar Musulmin Amurka a karkashin jam’iyyar ta Democrat wato AMDC.

Ta kan kuma yi yunkurin ganin ta ga Musulmin Amurka sun samu wakilcin da ya dace a duk fadin kasar.

An dai kafa kungiyar ta AMDC ce bayan harin ta’addanci da aka kawowa Amurka a shekarar 2001 na watan Satumba domin kare sukar da Musulmi ke sha da kuma shigar da Musulmi cikin siyasar Amurka.

“A wancan lokaci, tsoron da ake nunawa akanmu ya yi yawa sosai.” Sarwat ta ce.

Sai dai abinda ya wakana tsakaninsu da mutumin nan a cikin jirgi, ya kara nuna mata cewa har yanzu akwai wannan fargabar da ake nunawa akan Musulmi.

Kuma akwai bukatar Muslumin Amurka su yi maza-maza su kara cusa kansu a cikin harkokin siyasar kasar domin su rika sauya irin kallon da ake wa Musulunci.

GABA DAI, GABA DAI

Kungiyar ta AMDC an kafa ta ne a shekarar 2004 da reshen farko a jihar Texas, amma Sarwat ta ce yau akwai rasssa har 79.

Kuma ganin yadda aka samu karuwar Musulmin da suka halarci babban taron jam’iyyar Democrat a Philadelphia, akwai yuwuwar za a kara samun wasu rassa nan ba da jimawa ba.

Daga nan mu kan yi rijistar karin wasu rassa, saboda haka nan da shekaru hudu masu zuwa muna fatan mu kasance a kowane sako na kasar nan.” In ji Sarwat.

Wakilan wannan kungiya, sun gana ne na tsawon sa’oi hudu gabanin a zabi Hillary Clinton, kuma za su ci gaba da yakar manufofin Donald Trump, wanda kalamansa suka jefa fargaba a zukatan Musulmi.

Burin dai a cewar Sarwat shi ne a ci gaba da samun karin Musulmi da za su rika fitowa takara kuma su samu nasara.

Wannan shi ne burinmu, mu ga cewa mun habaka harkokin AMDC, domin mu ga cewa mun zama wadanda za a dama da su a karkashin jam’iyyar ta Democrat.” Sarwat ta ce.

Sai dai ta amince cewa akwai wasu da ba sa goyon bayan hangenta kan wannan batu.

“Akwai wadanda su ke tunanin samu Musulmi a jam’iyyar ma zai iya janyowa jam’iyyar bakin jini.”

Amma kuma ta kawo misalai da zabin da aka wa dan majalisar dokoki Keith Ellison a Minnesota da kuma ‘yar majalisa Andre Carson a Indiana, a matsayin wata alama da ke nuna cewa ana samun sauyi.

Sai dai wata damuwa ita ce yadda za a yi sa Musulmi su yi rijista da kara masu kwarin gwiwa da kuma kasancewa sun zamanto masu shaukin zuwa su kada kuri’a.

“Amma a hankali mutane na kara shiga kungiyar, mutane kuma na kara kusantar wannan manufa ta mu.”

DALILAI DA DAMA

Cibiyar bincike mai suna Pew, ta yi kiyasin cewa akwai akalla Musulmi miliyan 3.3 a duk fadin Amurka, wato kashi daya ke nan na adadin yawan al’umar kasar.

Ana kuma sa ran wannan adadin zai ninku nan da shekarar 2050.

Musulmi na daya daga cikin al’umomin da ke saurin karuwa a Amurka, amma da yawansu da ke da damar yin zabe ba sa yi.

Bai laifin gwamnatin Amurka ba ne,” in ji Tahir Ali, na gamayyar kungioyoyin Musulmi.

Ya kara da cewa wasu dalilai sun hada da rashin amincewa da tsare-tsaren gudanar da zaben, wanda su ke mai kallon ya saba ka’ida, yayin da wasu ke ikrarin ana magudi.

Wadannan in ji Ali, na daga cikin dalilan da ya sa Musulmin da suka yi kaura zuwa Amurka suka zama ‘yan kasa kuma suke da damar yin zabe, ba sa kada kuri’unsu ranar zabe.

“Ya zama dole mu wayar musu da kai cewa yanayin zabin akwai adalci a ciki, sai mun kara fahimtar da su yadda ake lissafin kuri’un matasa, mata saboda su fara tunanin cewa wannan dama ce da za su fito idon duniya.” Ali ya kara da cewa.

Ita kuwa Sarwat cewa ta yi, a lokuta da dama, kada kuri’a ba shi ne abinda ke gaban baki mazauna Amurka ba.

“Da yawa daga cikin baki za ka ji su na cewa, ba su samu nutsuwar da za su yi zabe ba, saboda dalilai da suka shafi kula da iyali, rainon yara, domin mafi yawansu al’adunsu ke nan."

Hakan kuma ya ke sa, damar yin zabe ke fadawa kan ‘ya’yansu, kamar irinsu Noman Khanani.

“Idan ka lura za ka ga cewa ‘ya’yan baki Musulmi ne ke yin zabe, yawancinsu za ka ga irin shekarun mu ne da muka dan haura 20 da kuma wadanda suka shiga 30, wanda haka ya ke da wahalar ayi hasashe, amma dai nan da wasu shekaru masu zuwa kamar biyar zuwa goma, za ka ga karin masu kada kuri’a a al’umar Musulmi.” In ji Khanani.

ALKALUMAN ZABEN FARKO

Wani zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a juhohi shida, wanda Majalisar Musulmin Amurka ta CAIR ta gudanar a watan Maris, a lokacin zaben gandu na “Super Tuesday”, ya nuna cewa kusan kashi 46 na Musulmi sun zabi ‘yar takarar Democrat Hillary Clinton a maimakon kashi 11 da suka zabi dan takarar Republican Donald Trump.

Wani abu kuma da sakamkon wannan bincike ya nuna shi ne, Musulmin da suka manyanta sun fi zabar Clinton yayin da matasa suka fi maida hankali kan Sanata Bernie Sanders na jihar Vermont.

Kuma Noman Khanani na daya daga cikinsu.

Na sabon shiga ne a wannan harka ta zabe, dalilin kawai da ya san a shiga harkar zabe shi ne irin ra’ayi nay a yi daidai da na Bernie Sanders.” In ji shi.

Kuma ya ce bashi kadai ne mai irin wannan ra’ayi ba a tsakanin Musulmi.

“Ina ganin kamar Musulmi da yawa sun shiga harkar zabe ne saboda ‘yan takara irinsu Bernie Sanders, wanda ya fi kare manufofin Musulmin Amurka fiye da kowane dan takara.

Yanzu dai babu wanda ya san ko Musulmi masu goyon bayan Bernie Sanders za su zabi Clinton, amma wani abu da zai iya taimakonta shi ne idan ta kwadaitar da Musulmi tsofaffi da ke mara mata baya su fita su kada kuri’unsu a watan Nuwamba.

HANGEN NESA

Yayin da Sarwat Husain ta zagaya da idanunta cikin babban dakin taron da kungiyar AMDC ke ganawa, ta lura cewa, mafi yawan matsan da ta ke kallo, kamar su Noman Khanani da suka kasance wakilai, wannan ne karon su na farko a irin wannan taro, wadanda kuma Sanders ne ya janyo hankalinsu.

Amma kuma hangen ta ya wuce na zaben watan Nuwamba, domin ta na fatar nan gaba za a samu wani dan takarar majalisar dokoki daga cikinsu.

Sai dai kowane dan takara na bukatar goyon baya, kuma a takara irin wannan, kowace kuri’a na da matukar muhimmanci.

Sarwat ta kara da cewa, baya ga farin jinin dan takara, neman hadin kan Musulmi Amurkawa ka iya kara cusa su cikin harkokin siyasar kasar.

Shiga harkar siyasa, tamkar ibada ce a Musulunci, akwai bukatar ka bautawa kasar da ke zaune ta kowane fanni.” In ji Sarwat.

Da a ce shekaru da dama ne da suka gabata Sarwat ta yi karon-batta da mutumin nan na cikin jirgi, da ta tunkari lamarin ta wata hanya daban, amma yau da gobe, ya sa ta goge kan yadda za ta tafiyar da irin wannan lamari kamar yadda ta yi.

“Idan irin hakan na faruwa akai-akai, hakan sai ya sa ka kara samun kwarin gwiwa.

Sannan ta ce akwai bukatar Musulmin Amurka su tashi cikin gaggawa domin samun wakilci daga al’umarsu, wacce na daya daga cikin al’umomin da ke bunkasa cikin gaggawa a Amurka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG