Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Taimakawa Kananan Mawaka


Abdul'aziz Saminu
Abdul'aziz Saminu

Kungiyar fasahar mawaka dake Kano Nijeriya tace tana taimakawa mawaka masu tasowa ko wadanda suke son fito da wakokinsu na farko ta hanyar taimaka musu wajen fitar musu da wokokinsu tun daga rubutu har zuwa fitar da shi.

Abdulaziz Saminu Abdulaziz Dan Hausa, mai zama welfare officer na kungiyar ne ya bayyana haka a zantawarsu da wakiliyar DandalinVoa, Baraka Bashir, a Kano,

ya ce idan aka taimaka wa mawaki aka fitar masa da wakarsa toh kungiyar su na daukar wani kaso a cikin abinda aka samu.

Ya ce hakan na taimakawa masu karamin karfin domin tabbatar da sun cimma burinsu, sannan suna kuma taimakawa sabbin shiga masana’antar waka ta hanyar koya musu yadda ake shirya waka da fitar da shi.

Ya ce burin kungiyar dai duk wani mai fasaha a taimaka masa ta hanyar da zasu kware , sannan kungiyar na taimakawa mawaka wajen karamasu kwarin gwiwa akan sana’ar.

Yana mai cewa babban kalubalen da mawaka ke fuskantar a cikin al’umma shine tun da farko basu fahimci mecece waka ba , ana yi musu wani irin kallon a cikin al’umma wanda hakan na kawo nakasu ga wasu mawakan har ta kai su hakura da burinsu domin su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG