A yau Alhamis, Kamfanin Dillancin labaran kasar Korea ta Arewa KCNA, ya yi ikrarin cewa kasar ta yi nasarar gwajin sabon makami mai linzami kirar Ballistic da ake wa lakabi da SLBM a takaice, wanda za a iya harba shi daga jirgin ruwa mai tafiya a karkashin teku.
Kamfanin dillancin labaran kasar, ya fitar da wasu hotuna da suka nuna lokacin da makamin mai linzami yake fitowa daga ruwa, a wani abu da ke nuna alamun daga karkashin tekun aka cullo shi.
Hukumomin Japan wadanda suka nuna rashin jin dadinsu kan gwajin, sun ce makamin wanda aka harba shi a jiya Laraba, ya sauka ne a wani yankinsu.
Wannan gwajin makami na zuwa ne, sa’o’i bayan da Korea ta Arewan ta bayyana cewa za ta yi wani zaman tattaunawa kan batun nukiliyanta da Amurka a ranar Asabar da ke tafe.
Har ya zuwa yanzu shugaban Amurka, Donald Trump, bai ce uffan ba, kan wannan sabon gwajin makami da Korea ta Arewan ta yi.
Facebook Forum