WASHINGTON, D.C —
A wata hira da wakilin Muryar Amurka Ridwan Abbas, wasu dattawa kuma shugabannin kasuwar dabbobin sun bada dan takaitaccen tarihin kasuwar da kuma yadda harkokinta ke gudana.
A cewar su, akwai sauki a farashin wasu dabbobin duk da cewa jama'a na kokawa da tsadar da suka yi a baya-bayan nan.
A wannan kasuwa dai ana kai dabbobi daga kasashen Mali, Burkina Faso, Najeriya da jamhuriyar Benin. 'Yan kasuwar sun kuma yi kira ga gwamnati da ta sama musu matakan tsaro saboda akan yi musu sata.
Saurari cikakken shirin cikin sauti.