Kafar sadarwar rediyo taci gaba da zama mai tasirin gaske a birane da kuma yankunan karkara, inda jama'a kan saurari rediyo duk inda suke au suna tukin mota ko suna kan keke ko kuma suna sararawa.
Haka kuma a kshen da babu wadatar wutar lantarki, mutane kan dogara akan akwatunan rediyo domin samun labarai na sanin abubuwan da suke faruwa harma gandun daji.
Wannan rana da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don rediyo ta samu asalin ne daga fara sadarwar rediyo a alif dari tara da arba'in da shidda.