A Yemen 'yan tawayen kasar 'yan shi'a masu karfi, sun kammala daukan matakan tabbatar da juyin mulkin da suka ayyana a kasar, a cikin wani bayani da suka yi ta talabijin jiya jumma'a cewa, sun rusa majalisar dokokin kasar, kuma zasu kafa sabuwar majalisar zartaswar.
A cikin sanarwar da aka karanta a tashar talabijin tab kasar, 'yan tawayen da ake kira Houthi suka ce majalisar shugaban kasar mai wakilai biyar ita zata tafiyar da harkokin kasar da galibin jama'arta yan mashabar sunnni ne na tsawon shekaru biyu. Kungiyar tace zata kafa majalisar dokokin kasar mai wakilai 551 da zata maye gurbin wacce suka rushe, sanan sabuwar majalisar ita ce zata zabi sabuwar majalisar shugaban kasa.
Sai dai Amurka taki ta amince da shirin da 'yan tawayen suka gabatar jiya, tana mai cewa kudurin bai kunshi matakai da zasu magance rikicin siyasar da Yemen take fama dasu ba.
A birnin New York, kakakin babban sakataren MDD Ban ki-moon yace magatakardan MDD ya damu kan rashin shugabancin a Yemen.
Rikicin siyasar da Yemen take ta fama dashi na watanni ya jefa kasar cikin yamusti. Sannan rashin tabbas din ya kara tsanani saboda kasancewar reshen al-Qaida dake kasar.
An kammala shawarwari tsakanin 'yan tawayen Huthi da jam'iyun siyasar kasar ranar laraba data shige ba tareda an cimma wata yarjejeniya ba.