A cigaba da wasannin da akeyi na neman cin kofin kasashen Afirka 2017 (CAF) a kasar Gabon, Jiya an kece raini tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta kasar Senegal da Algeria inda aka tashi 2 da 2, Zimbabwe ta sha kashi a hannun Tunisia da kwallaye 4 da 2.
Bayan kammala wasan rukunin (B) kasar Senegal tana mataki na daya da maki 7, Tunisia tana mataki na biyu da maki 6, Algeria, a matsayi na uku da maki 2, Yayinda ita kuma kasar Zimbabwe, ke mataki na hudu da maki 1 don haka kasar Senegal da Tunisia sun samu hayewa zuwa zagaye na gaba.
A yau kuma rukunin (C) zasu gwabza a wasanninsu na ukku inda Morroco zata kece raini da kasar Ivory Coast. Togo zata fafata tsakaninta da RD Congo, da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.
A kasar Spain kuwa yau za'a fafata a wasannin Copa del rey 2016/2017, a matakin wasan kusa da nakusa da na karshe (Quater Final) tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Alaves da Alcorcon, a karo na biyu da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya da Nijar.
A karon farko ranar 18/1/2017 Alaves ta doke Alcorcon daci 2-0 a gidan Alcorcon.