Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mike Pompeo Yana Birnin Kabul Don Sasanta Tankiyar Siyasa


A yau Litinin sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa birnin Kabul, a wata ziyarar bazata, don kokarin sasanta tankiyar siyasa tsakanin shugaban kasar Ashraf Ghani da abokin hamayyarsa Abdulla Abdulla, da ke kokarin wargaza yarjejeniyar da Amurka ta jagoranta na sulhu da kungiyar Taliban a watan jiya.

Ghandi da Abdullah dai sun rantsar da kawunan su a matsayin shugabanin kasar, bayan wani zabe da aka gudanar mai cike da rudani.

Wannan tafiya tazo a dai-dai lokacin da shugabani a duniya suke takaita tafiye-tafiye saboda annobar Coronavirus. Duk kuwa da makonni da jigo a gwamnatin Trump ya yi Zalmay Khalilzad a Kabul din don ganin an dai-daita, amma abun ya ci tura, inda yake cewa “Abun da muke so shi ne shugaba Ghani da abokin takararsa Abdullah su cinma matsaya da za’a samar da gwamnatin Hadaka, wadda dukan bangarorin biyu zasu amince da ita.”

Wani babban jigo a ma’aikatar wajen Amurka ya shaidawa manema labarai cewar “Duka bangarorin biyu sun san da tazarar dake tsakanin su. Muna fatar zasu warware matsalar a yau.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG