Manajar Microsoft mai kula da kasashen Najeriya da Ghana, Ola Williams, ce ta sanarda hakan yayin rangadin duba kirkirarriyar basirar da kamfanin yayi a jihar legas a yau laraba.
“Ina mai farin cikin sanarda cewar mu a matsayinmu na kamfanin Microsoft dake Najeriya, zamu zuba jarin dala milyan guda nan da shekaru 2 masu zuwa domin baiwa ‘yan Najeriya milyan 1 horo akan dabarun sarrafa kirkirarriyar basira ,” kamar yadda Williams ta sanar cikin shauki.
Ta kara da cewar da wannan horo, matasan najeriya zasu samawa kawunansu hanyar samun kudin shiga mai dorewa tare da yin gogayya da takwarorinsu a matakin duniya.
Rangadin kirkirarriyar basirar na Microsoft ya tattauna a kan makomar fasahar da kuma irin damammakin da za ta samar a fannonin rayuwa daban-daban.
Dandalin Mu Tattauna