Shahararrun kamfanonin kimiyya da fasaha na Amurka sun fara shiga kasashen Afrika don cirani. Kamfanonin da suka hada da Microsoft, Facebook da Uber. suna kashe makudan kudade wajen koyar da mutanen nahiyar sanin makamar na’urorin zamani.
Kamfanin Microsoft ya shirya don zuba jari da suka kai kimanin dala miliyan $100, kwatankwacin naira miliyan dari ukku da sittin, don bude wata cibiyar kimiyya da fasaha a Afrika da za a yi su a Najeriya da Kenya cikin shekaru 5. Wannan itace cibiya ta farko da Microsoft zai bude a nahiyar Afrika.
Makomar kimiyya da fasaha ta duniya tana kasashen Afrika, nan bada jimawa ba Afrika zata zama kangaba wajen kirkiro sababbin manhajoji da duniya za tayi alfahari da su.
Microsoft ta ce hakan yasa muka fara samar da duk wasu abubuwa da za a bukata a nan gaba wajen ciyar da duniya gaba daya, shi yasa muke bude cibiyoyi a nahiyar.
Kamfanin na Microsoft ya bayyana cewar nan bada jimawa ba, zai dauki ma’aikata daga wadannan kasashen da zasu kai inginiyoyi 100, a bangaren kashe kudi kuwa zasu kashe fiye da dala miliyan $100 akan ginin ofishin su, albashin ma’aikata da jin dadinsu.
Shi kuwa shugaban kamfanin Facebook Mack Zuckergerg tun a shekarar 2016 ya ziyarci Najeriya, inda ya fara kashe makudan kudade a kasar, wanda kuma ya tabbatar da cewar zasu cigaba.
Facebook Forum