Fadar gwamnatin Najeriya ta ba da labarin cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi wata tafiyar da za ta kai shi har 17 ga watan gobe kafin ya juyo Abuja.
Tafiyar da ta zo nan take bayan dawowar shugaban daga taron tattalin arzikin Afirka a birnin Sochi na Rasha, za ta kai shugaban wani taron tattalin arzikin a birnin Riyadh na Saudiyya.
Bayan kammala taron na Riyadh da zai samu halartar shugaban Kenya Uhuru Kenyatta karkakashin jagorancin Yarima Mohammad Bin Salman, shugaba Buhari zai yi umrah daga nan sai ya wuce wani balaguron da aka ce kebantacce ne zuwa London.
A baya dai an saba ganin shugaban na tafiya hutu ko ganin likita a London, inda hatta lokacin da ya ziyarci Amurka sai da ya biya ta London din kafin dawowa gida.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya sha rubuta wasiku na nuna rashin jin dadin yadda shugaban ke gudanar da lamuran mulki da hakan ya sanya masu hamayya da gwamnatin buga misali da hakan da nuna damuwa cewa tafiye-tafiyen shugaban sun yi yawa.
A martaninsa kan wasikun Obasanjon, mai taimakawa shugaban kan labaru, Garba Shehu, ya ce Obasanjon ne ba ya zama don haka bai fahimci shugaba Buhari ba.
Mutane dai sun kasu kashi biyu tsakanin masu nuna ribar tafiye-tafiyen ga tattalin arziki da masu cewa ana kashe makudan kudi kan tafiye-tafiyen.
Sai dai matashin dan kasuwa a Abuja Yusuf Ahmad ya ce ba wata fa’ida ta zahiri da a ka gani.
Sai dai dan siyasa Abubakar Sadik Ahmad ya ce akwai fa'idar tafiye-tafiyen ga tattalin arziki.
Kwanan nan gwamnatin ta ba da umurnin takaita tafiye-tafiyen ‘yan majalisar zartarwa da ma tawagar kar ta wuce mutum hudu har da ministan don rage kashe kudi ba riba.
Saurari rahoton wakilinmu Nasiru Adamu El-hikaya daga Abuja:
Facebook Forum